Hadakar kalmomin soyayya

Hadakar Kalomin Soyayya A-Z A = Agaskiya ina matuqar sonki saudat wlh sosai sosai fiye da yadda kife ke son ruwa hmm to dan yi murmushi mana (ana furtawa masoyiya irin kalamannan cikin murmushi me dauke da kallon qauna,mace tana iya ha dawa da hawayen qauna dan raunata zuciyar masoyinta da qara so da qauna) B = Babban burina naga na mallake wannan tauraruwar dake haskawa ,hmm zainab kinsan me kuwa ? Wlh ban dawani buri irin naga na aureki. C = Cutar sonki batada magani agurin likita saidai ke,cancantarki ce tasa hakan zurfa'a ina me tabbatar miki bazan taba jabaya a soyayyarkiba kece farincikin raina burun zuciyata zurfa'ah tawa wai dan Allah zurfa'ah wanna irin so nake miki haka? Pls fadamin dan Allah D = Dadadan kalamanki kan sanyaya min rai,tamkar ruwan sanyi lokacin buda baki E = Eh mana na aureki shine burin zuciyata,burin zuciyata kuwa shine farin cikin raina ,farin cikin raina kuwa shine hasken rayuwata Nafisa wlh ina matuqar so naga kinzama amaryata. F = fito na fito dan a yaune zan fidda gwanata, G = Gashi amshi masoyiyata wlh na baki zuciyata dukka kisarrafata yadda kikeso H = hanzarta abar qaunata ki tsamoni da dadaden kalamanki ma so sanyaya zuciya daga cikin tekun sonki , I = Irin dabi'unki khadija gaskiya ababan sone danhaka na amunta dake nayaba da hankalinki dan shike kara min sanki azuciyata J = Jinjina ga ma abociyar kyawu kyakykyawa mai kyan hali K = kokinsan zainb Allah yaimiki ni imar kyau da hankali gamida tsan tsar nutsuwa hmm nikam nagodewa Allah dayabani ke zainab L = Lamuninki kawai agareni agareni husnah wlh nasarace a arayuwata pls daure ki amunta dani 100% kamar yadda na amunta dake 100% M = masoyinki abun qaunarki,me qaunarkikuwa shi ya can canta daya mallakeki. Haba jamila ta pls sai i'love you N = nasan bakida shakku ko tan tama gameda sonda nake miki kubra na qara jaddada miki wlh ba ranar dazatazo najuyanki baya insha Allah tawan R = rayuwa da masoyi maidadi ,safnah kece masoyiyata ta asali matukar bansameki ba to rayuwa tabaci S = SOnki qawanyane ya sarqen zuciyata, ganin ki kadai ke warware ta gimbiyar mataye, T = Tafiyarki dabance gwana tagwanaye abar kwaikwayon yanmata,gaskiya saudat wlh kin iya kwalliya essalen U = Uziri zakiyimin masoyiyata nakan rasa kwanturol dazarar naji dadadan kalamanki masu dake da wani sauti me ratsa zuciyata ,kai lallai nayarda so Aljannar duniya ni gatawa na samu hmm Allah yabani ke hafsat W = wajibine nayiwa Allah godiya bisa kyautar ma abociyar hankali da tausayin da yabani ,haqiqa MAIMUNA nayi dace da samunki masoyiya Y = yaune nake so na baiyyana miki irin son danake miki ,kisani shamsiyya wlh bani da wasu kalmomi ko ma auni dazasu iya bayyana son danake miki ,nidai ina sonki ,ina qaunarki ,kece burin zuciyata ,farin cikin raina cikar mafarkina wlh sham siyya matuqar ba zaki'iya qairga ruwan tekuba to bazaki iya qididdi ge son da nake miki ba Z = ZUCIYATA kullun tana tabbatar min cewa baranar da zatazo naji araina nayi nadamar zabarki Maijidda wlh nagama amunta dake tuni na mallakan ki zuciyata pls daure kibani taki . Soyayya gamanjini, yan uwa wadannan wasu hadakane na kalaman soyayya ,dan nishadantar daku kawai, aciki zakuga akwai kalaman qarfafa zuciya,na raunana zuciya, na mallake zuciya ,na tabbatar da soyayya,da shauran su.dafatan kunji dadi Allah yaqara danqon soyayya ,wanda bai da budurwa Allah yabashi mai ita Allah yasa ayi soyayyar gaskiya da amana http://sulemanyahyaringem.blogspot.com/

Comments

Popular posts from this blog

Sinadaran Kalaman Soyayya