Sinadaran Kalaman Soyayya Sinadaran Kalaman Soyayya Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan karon in sha Allah za mu tattauna kan sinadaran da suke kara dandano da zakin kalaman soyayya tsakananin masoya. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin. 1.Sarrafa Murya Wata babbar ka’ida da take kara inganci da tasirin kalaman bayyana soyayya tsakanin masoya ita ce, yanayi da sigar da kalaman ke fita su isa kunnen mai sauraren su. Dole sai masoya sun rika sarrafa murya wajen bayyana shaukin kaunarsu ga juna; kowane kalami da irin sigar muryar da tafi dacewa da shi: • Kalaman nuna so da kauna ana furta su garwaye da shaukin bege, cikin bayyanannun kalmomi, wata sa’in ana iya furta su cikin yanayin wake, ko a siririntar da murya ko a nauyaya ta don ta yi daidai da lokaci da kuma yanayi. • Kalaman tausayawa, suna bukatar a tausasa murya wajen furta su, a cakud...
Comments
Post a Comment
Alhamdulillah alakullihalin